Allah kadiran ala man yasha’u, wani hatsarin mota da ya auku a jihar Katsina ya rutsa da Liman da kuma wasu matsa bakwai ‘yan unguwar Kurna ta jihar Kano a Katsina.

Kamar yadda Freedom Radio ta ruwaito, Mai unguwar Kurna Tudun Bojuwa shi ne ya tabbatar da aukuwar lamarin.


Inda ya ce, har yanzu ba a gama tantance adadin mutanen da hatsarin ya shafa ba.

Almajirin babban limamin yankin, Malam Iiiyasu Nagurasu shi ake daura wa aure a Katsina, matasan unguwar sun gamu da ajalinsu ne ranar Laraba a kan hanyarsu ta zuwa Katsina daurin auren.

Shi ma limamin, Malam Iliyasu ya rasa ransa a hatsarin, har yanzu ana nan ana dakon a iso da gawarwarkin domin yi musu sutura kamar yadda addini ya tanadar.
Labari na baya Labari na Gaba