A ranar litinin, 13 ga watan Disamba, Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ya yi wata ganawar sirri da Shugaba Buhari a  Aso Villa.

Gwamnan Sokoto, Tambuwal

Bayan gwamnan ya yi wa Buhari cikakken bayani akan matsalar rashin tsaro a Sokoto, ya kuma yi kira ga Buharin da ya sanya dokar ta baci a kafitanin yankunan da ke fama da matsalar rashin tsaro a fadin jihar.

Kazalika Tambuwal din ya kuma bukaci shugaban ya baiwa jami’an soji cikakkiyar damar gudanar da aikinsu ba tare da kakkautawa ba a kaf yankunan da lamarin ya shafa.

Wannan rahoton ya fito ne daga cikin wata sanarwa da Muhammad Bello, mai baiwa gwamnan shawara kan harkokin yada labarai ya fitar.

Idan ba ku manta ba, kwanaki kadan da suka wuce wasu ‘yan bindiga suka kone wasu matafiya 40 da doriya a jihar Sokoto.

Lamarin da ya jawo cece-kuce a kafafen sada zumunta da kuma zanga-zangar #NoMoreBloodShed da aka gudanar a kafitanin Arewacin Najeriya.

Har yanzu dai jihar ta Sokoto na cigaba da fuskantar kalubalen tsaro.
Labari na baya Labari na Gaba