Sarauniyar kyau ta 44 ta wannan shekarar, Shatu Garko ta bayyana yadda ta samu nasarar shawo kan mahaifinta har ya amince ta shiga gasar.

Shatu Garko
Shatu Garko

Shatu, budurwa mai shekaru 18  ta zamto mace mai hijabi ta farko da ta taba lashe gasar tun farkon fara ta a shekara ta alif 1957.

Sarauniyar kyan ta 2021 ta bayyana hakan ne yayin zantawarta da jaridar The Punch.

“Mahaifina ne baya so, amma mahaifiyata tana goyon bayana ta kuma nusar da ni cewa abin ba wani mai wahala bane.”

“Mahaifina ya damu ne saboda kada su tilasta ni in cire hijabi ko saka kayan da za su fito da surar jikina ko su cire ni saboda kin yin shigar da su ke so. Ni da mahaifiyata muka taru muka bashi hakuri sannan ya amince, da amincewarsa na yi gasar.”

A cewar Shatu, mutane da dama sun kalubalanci shigarta gasar, wasu har kira suke ta koma makaranta maimakon shiga gasar.

“Eh, ba ‘yan arewa kadai ba, har wasu daban sun caccake ni. Wasu sun dinga cewa zan bata sunan gasar. Akwai wadanda su ka dinga cewa zan kai ‘yan Boko Haram ko kuma makiyayan Fulani cikin gasar. Kawai share su nayi.”

Ta kara da bayyana yadda lokacin da ta shiga gasar ba ta yi tunanin za ta ci nasara ba amma ta jajirce da kwarin guiwa har ta samu nasarar.

Garko ta lashe gasar ne a ranar Juma’a, 17 ga watan Disamba inda ta kasance mace ta farko daga Kano da ta bige mutane 17 ta ci nasarar. 

An yi gasar ne a jihar Legas kuma ta samu kyautuka kamar N10m, zama a katafaren gida na shekara daya, sabuwar mota da kuma damar tallata kaya da dama.
Labari na baya Labari na Gaba