A yau talata, Shugaban majalissar dattawa, Ahmad Lawan ya karanto wata takarda da Shugaba Buhari ya rubuta wa zauren, inda ya bukaci nada sabon minista daga jihar Taraba.

Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya, Buhari.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika sunan wani ‘dan jihar Taraba, Mu’azu Jaji Sambo gaban majalissar dattawa domin ta lamunce ya nada shi sabon minista.

Sannan Buharin ya bukaci majalissar dattawan ta yi binciken kwakwaf, ta tantance Mu’azu Jaji sannan ta kuma tabbatar da shi domin a nada shi a matsayin minista.

Sai dai, kawo zuwa yanzu manema labarai ba su san ministan wanne fanni za’a nada Mu’azi Jaji ba.
Labari na baya Labari na Gaba