Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sha alwashin kawo karshen dukkanin ta’addancin ‘yan bindigar da suka addabi Arewa maso Yammacin Najeriya

Shugaban ya ce rundunar soji za ta ci gaba da daukar matakai masu tsauri kan ‘yan bindigar da ke addabar yankin Arewa maso Yamma.

Buhari ya yi wannan alwashi ne a ranar Alhamis yayin da yake bude cibiyar ilmantarwa ta Muhammadu Indimi da kuma taron kasa-da-kasa a jami’ar Maiduguri.

Muhammadu Buhari
Muhammadu Buhari

Shugaban wanda ya ce ya ji dadin yadda tsaro ya inganta a yankin Arewa maso Gabas, ya koka kan ayyukan ‘yan bindiga a yankin Arewa maso Yamma.

Shugaban ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi wa gwamnatinsa hukunci bisa la’akari da yanayin da ake ciki a lokacin da aka rantsar da shi da kuma halin da ake ciki a yanzu.

Idan ba ku manta ba jiya Alhamis, 23 ga watan Disamba, 2021, Buhari ya kai ziyara jihar Borno, sai dai da isarsa jihar dakarun Boko Haram/Iswap suka harba rokoki 3 a sassa daban-daban cikin jihar.

Labari na baya Labari na Gaba