Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ceci dukkanin Gwamnonin Najeriya daga jin kunyar al’ummar da suka zabe su.

Badaru Abukakar Talamis
Gwamnan Jigawa, Badaru Abukakar

Badaru Abubakar, Gwamnan jihar Jigawa ne ya bayyana hakan a wurin kaddamar da aikin titin da ya hada Kano da Maiduguri na biyu har ya biyo ta Shuwarin-Azare a jihar Jigawa.

A cewarsa, ba don goyon baya da taimakon shugaba Buhari ba da kawo yanzu gwamnonin jihohi 36 ba su samu nasarorin da suka samu ba.

Badaru Abubakar ya bayyana cewa, in ba don goyon boyon bayan Buhari ba to zai yi wuya gwamnoni su cika dukkan alkawurran da suka dauka wa al’ummarsu kafin zabe.

Ya yi nuni da cewa, a lokacin da aka fara rantsar da gwamnoni, kusan jihohi 24 zuwa 26 ba sa iya biyan albashi, amma shugaban ya goyi bayansu ya ba su wuri Naira biliyan 10 don fara yin ayyukan more rayuwa wa al’ummarsu.

Gwamnan ya ce gwamnatin tarayya ta biya jihohi dukkan kudaden da ake kashewa a titunan tarayya, kudaden Paris club da ake cirewa jihohi da kananan hukumomi, kuma a kwanakin baya ta amince da naira biliyan 18 ga jihohi 36 domin kara musu illar cirar lamuni.

"Idan ba tare da wadannan tallafi ba, ni da sauran Gwamnonin ba za mu iya tsayawa ba saboda kunya, tare da tallafin da muke bayarwa yanzu muna cika alkawuran da muka yi."

Don haka Badaru Abubakar ya bukaci ‘yan Najeriya da su yaba wa Buhari kuma su ci gaba da addu’ar Allah ya kawo karshen matsalar rashin tsaro a kasar.

Labari na baya Labari na Gaba