Shararren shugaban ‘yan bindigar nan na jihar Zamfara, Muhammadu Bello Turji ya yi alkawarin aje makami da shi da tawagarsa da mika kai ga hukuma muddin gwamnatin za ta haramta kungiyoyin sa kai kwata-kwata.

Hakan ya fito ne a cikin wata takardar neman sulhu da gwamnati da shugaban ‘yan bindigar na Zamfara ya fitar domin a yi sulhu.

Bello Turji
Bello Turji

Ga abinda ya fadi cikin takardar a cikin sharadi na farko, wanda a cikinsa ne ya bukaci gwamnati ta soke kungiyar ‘yan sa kai domin kawo zaman lafiya cikin kasar Najeriya baki daya.

“Kashe-kashen da ake yi na al’umma wadanda basu ji, basu gani ba, ya kai karshe, domin ‘yan bindiga su kashe, ‘yan sa kai su kashe, kuma jami’an tsaro su kashe, da kuma daukar mutane domin karbar kudin fansa, to Insha Allahu (S.W.T) za’a kai karshenshi da yardar ubangiji Allah, matukar gwamnati za ta soke kungiyar ‘yan sa kai, Insha Allahu za mu aje makamai duka.”

To, shin ko gwamnati za ta amince wannan kuduri na ‘dan bindiga Bello Turji? Ku biyo mu domin jin abinda mahukunta za su ce game da wannan sharadi.
Labari na baya Labari na Gaba