A can Benin, jihar Edo wani mutum wanda ya dawo gida daga kasar Ghana ya tsere bayan ya yiwa budurwarsa kisan gilla a jajibirin Kirsimeti.

Aika Aika
Aika Aika

Mutumin mai suna Osas yanzu haka dai yana kan gudu bayan kisan budurwarsa mai suna Elohor Onioroso a Benin.

An ce lamarin ya faru ne a kusa da unguwar Egor da ke babban birnin jihar, kamar yadda Vanguard Nigeria ta ruwaito.

A cewar kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Bello Kontongs, mahaifin mamacin William Oniorosa ne ya kai rahoton lamarin ga ‘yan sanda kuma ana ci gaba da gudanar da bincike domin kamo wanda ake zargin.

 Ya ce: “Wanda ake zargin sunansa Osas kuma ba a san sunan mahaifinsa ba shi, mahaifin Elohor Oniorosa, William Oniorosa ne ya kai rahoton faruwar lamarin ga ‘yan sanda.”
   
“Ana ci gaba da bincike yayin da wanda ake zargin ke kan gudu. Lamarin ya faru ne a ranar 24/12/2021, "in ji SP Bello.

An tattaro cewa wanda ake zargin ya dawo ne daga Ghana a makon da ya gabata, inda ake zargin ya yanka budurwar tasa a Benin.
Labari na baya Labari na Gaba