Wata motar bas cike da ‘yan bautar kasa ta kama da wuta yayin da ta ke tsaka da tafiya a sansasin NYSC da ke jihar Delta.

Bas din 'yan NYSC da ta kama da wuta
Bas din 'yan NYSC da ta kama da wuta

Wasu bayanai da suka iso teburin watsa labarai na Dan Lanjeriya sun tabbatar da cewa wata motar bas da ke dauke da ‘yan bautar kasa ta fashe a kan hanyarta ta daga sansanin masu yi wa kasa hidima na Najeriya, reshen jihar Delta.

Wadanda lamarin ya faru a gaban idanunsu sun tabbatar da cewa, motar bas din tana jigilar ‘yan bautar kasar ne zuwa wurin aikinsu yayin da ta kama da wutar.

Kalli hotunan yadda lamarin ya faru:
Motar bas din na kan hanyar zuwa Warri, bayan masu yi wa kasa hidimar sun gudanar da aiyukansa kafin ta kama da wuta a kan hanyar.

Wani wanda lamarin ya auku ya na cikin motar ya bayyana cewa yawancinsu sun shagaltu da wasu abubuwan a cikin motar.

Sai dai ba su san da tashin gobarar ba, sai da direban ya fara ihu tare da neman kowa da kowa ya yi gaggawar ficewa sannan su ka ankare da abinda ke wakana.
Labari na baya Labari na Gaba