An samu nasarar dawo da wutar lantarki a cikin birnin Maiduguri da kewayenta bayan mazauna birnin da kewayensa sun shafe shekara guda cif cikin duhu.

Idan ba ku manta ba, a banan nan ‘yan tada kayar baya suka lalata akalla tasoshin wutar lantarki 10 da ke kan hanyar Maiduguri zuwa Damaturu, lamarin da ya jefa babban birnin jihar cikin duhu.

Gwamnatin tarayya da kuma gwamnatin jihar Borno sun sha yin kokarta gyaran layin wutar mai karfin 330kv amma hakansu bai cimma ruwa ba.

Cikin sa’a ma’aikatar gidaje da makamashi ta jihar tare da hadin gwiwar hukumar kula da wutar lantarki ta karkara su ka samu nasarar sake farfado da layin wutar cikin kwanaki 20.

Da yake mika layin Damaturu-Maiduguri mai karfin 330KV ga Yola Distribution Company, Kwamishinan Makamashi, Yuguda Vungas ya ce an samu nasarar ne bayan umarnin da Gwamna Babagana Zulum ya bayar na maido da wutar lantarki a Maiduguri da kewayenta cikin kwanaki 30.

Kwamishin ya yi kira ga Yola Distribution Company da su gaggauta fara raba wutar su kuma tabbatar da al’umma na samun isasshiyar wutar lantarki

Kalli hotunan yadda ake maido da wutar:

An kawo wuta a Borno

Usman Wakta da Hajiya Zainab Hassan

An Kawo Wuta a Maiduguri

Yola Distribution Company

Da suke mayar da martani, manajojin kasuwanci na ofishin Bulunkutu da Yerwa na Kamfanin, Mista Usman Wakta da Hajiya Zainab Hassan sun yaba da kokarin Gwamnan inda suka ce za a raba Megwatts 18 da aka samu ga duk al’umma inda za su rinka samun wuta tsawon sa’o’I 6 a kullum.

Da manema labarai suka tuntubi mazauna Maiduguri, sun bayyana jin dadinsu ga Gwamnan bisa cika alkawarin da ya dauka, inda suka ce hakan zai ci gaba da bunkasa harkokin kasuwanci a jihar.
Labari na baya Labari na Gaba