Jami'an ‘yan sanda sun kama wasu miji da mata bisa zargin sayar da jaririnsu ‘dan wata daya ga wata mata a kan kudi ₦50,000 kacal a jihar Ogun.

An kama ma’auratan ne a ranar Alhamis a unguwar Ilara da ke Ode Remo,a karamar hukumar Remo ta Arewa a jihar Ogun.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi, ya shaida wa manema labarai a ranar lahadin da ta gabata cewa, an kama ma’auratan Onyebuchi Eze da matarsa Oluchi Eze ne biyo bayan wasu bayanai da jami’ai suka samu a hedikwatar ‘yan sanda ta Ode Remo.

Onyebuchi Eze da Oluchi Eze
Onyebuchi Eze da Oluchi Eze

A cewarsa, ma’auratan mazauna titin Ayegbemi, Iiara Remo da son ransu suka siyar da jaririnsu ‘dan wata daya ga wata mace a halin yanzu.

Sakamakon haka, DPO na Ode Remo, CSP Olayemi Fagbohun, ya ce baiwa jami’ai masu bincike a yankin umarnin bincikawa tare da damko wadanda ake zargin.


Da ake yi masa tambayoyi, Oyeyemi ya bayyana cewa wadanda ake zargin sun amsa cewa “wata mata Misis Ruth Obajimi ce ta hada su da mai siyan jaririn wadda har yanzu ba a san wacece ba” a ranar 14 ga watan Disamba.

“Sun ci gaba da cewa matar ta gaya musu cewa ta fito ne daga ofishin kare hakkin dan Adam kuma za ta taimaka musu wajen renon yaronsu.

“Sai matar ta ba su kudi naira 50,000 sannan suka mika mata jaririn duk da ba su san ta daga ofishin kare hakkin ‘dan adam ba,” in ji wanda ya dauki hoton ‘yan sandan, inda ya kara da cewa ana kokarin kama matar don kwato jaririn.

A halin da ake ciki, kwamishinan ‘yan sandan jihar, Lanre Bankole, ya bayar da umarnin a gaggauta mika ma’auratan zuwa sashin yaki da fataucin bil’adama da bautar da yara na CIID na jihar domin ci gaba da bincike.

Bankole ya kuma bayar da umarnin gudanar da gagarumar farautar wadda ta sayi jaririn. Kamar yadda jaridar DailyPost ta ruwaito.
Labari na baya Labari na Gaba