Jami’an ‘yan sanda da ‘yan banga na yankin Oleh da ke karamar hukumar Isoko ta Kudu a jihar Delta sun kama wani matashi dan shekara ashirin da shida mai suna Davidson Odigho a zagayen Irri a Oleh.

David Odigho | Hoto: dailypost.ng
An kama wanda ake zargin ne bisa zargin rashin nasara a  yunkurinsa shi da abokan aikinsa yayin yin garkuwa da wata mata da ta dawo gida daga Turai.

Hakan na zuwa ne yayin da sauran ‘yan kungiyar masu garkuwa da mutanen suka tsere daga wurin da lamarin ya faru a cikin wata farar motar kirar Hilux ba tare da lambar rajista ba.

Rundunar ‘yan sandan ta kuma kwato bindiga kirar AK47 daya, harsashi mai tsawon mita 7.62  guda goma sha tara (19), da mujalla daya, bindigar famfo daya da harsashi guda ashirin da shida (26) da aka boye a cikin jakar buhu aka binne su a harabar gidan wanda ake zargin.

Masu garkuwa da mutanen sun samu gagarumar cece-kuce tsakaninsu a yunkurinsu na yin garkuwa da mutumin da ya dawo daga Turai wanda hakan ya sanya mazauna garin suka sanar da ‘yan banga.

An kama daya daga cikin wadanda ake zargin ne a wani operation na tsanaki karkashin jagorancin shugaban 'yan sanda na yankin, DPO Oleh bayan ya samu kira daga ‘yan banga.

Rundunar ‘yan sandan jihar Delta, CP Ari Muhammed Ali ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na ‘yan sandan, DSP Bright Edafe.

“Da aka yi masa tambayoyi, wanda ake zargin ya amsa cewa yana cikin ’yan kungiyar da suka yi garkuwa da matar mai shekaru 63 a ranar 30/11/2021 kuma ya watsar da ita a lokacin da suka lura cewa ‘yan sanda  na kokarin damke su." Kamar yadda jaridar DailyPost ta ruwaito.

A cewar DSP Edafe, “Wanda ake zargin ya jagoranci ‘yan sanda zuwa gidansa inda aka boye bindiga kirar AK 47 guda 19, harsashi mai girman millimita 7.62, mujalla daya, bindigar fanfo daya da kuma harsashi guda ashirin da shida (26) a cikin buhu. an kwato jaka aka binne a harabar.”

Ya kuma kara da cewa “ana ci gaba da farautar 'yan kungiyar da yanzu haka suna kan tserewa.”
Labari na baya Labari na Gaba