Rundunar  ‘yan sandan jihar Osun ta bayyana sunan jami’inta wanda ya bindige Kabiru Babai a Ota Efun da ke jihar ta Osun.

Shi dai Kabiru Babai ma’aikaci ne a wani kamfanin damfara mai suna Shekeenah Zelter Global Concept.

Sajan Samuel
Sajan Samuel tare da Abokin aikinsa

Wani jami’in dan sanda mai suna Sajan Moses Samuel shi ne ya bindige Kabiru Babai mai shekaru 33 har lahira a ranar Juma’a, 3 ga watan Disamba, 2021.

Rahotanni sun bayyana cewa, Sajan Samuel, ya harbe ma’aikacin damfarar a unguwar Ota-Efun da ke Karamar Hukumar Osogbo ta jihar Ogun.

Rundunar ‘yan sandan jihar Osuna ta tabbatar da cafke wanda ya aikata laifin.

Jami’ar hulda da jama’a ta rundunar ‘yan sandan jihar, Yemisi Opalola ce  ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar ga jaridar Daily Post a ranar lahadi.

Kakakin  rundunar ‘yan sandan jihar ya ce, “Rundunar ‘yan sandan jihar Osun a ci gaba da kokarinta na dakile duk wani nau’in rashin da’a da rashin sanin makamar aiki, ta kama tare da tsare dan sanda, Sgt Moses Samuel wanda ya harbe wani Malam Kabiru Babai  mai shekaru 33 a jiya, 3 ga Disamba, 2021 wajen Kobogbogboe/Ota-fun Area, Osogbo.”

"An fara gudanar da bincike da kuma ladabtarwa ga wanda ake zargin kuma za a gurfanar da shi a gaban kotu bayan an kammla binciken domin hakan ya zama izna ga sauran jami’ai.”

Ta kara da cewa kwamishinan ‘yan sandan, Olawale Olokode, ya jajantawa ‘yan uwa da abokan arziki tare da tabbatar wa jama’a cewa za a yi adalci a lamarin.
Labari na baya Labari na Gaba