Jami’ai sun kama wadansu daliban makarantar sakandire ‘yan shekaru 16 su uku bayan sun sha giya sun yi tatil suna kuma aikata lalata.

Daliban ‘yan makarantar Gagitu Mixed Secondary School da ke kasar Kenya, an cafke su ne a ranar Talata, 14 ga watan Disamba, 2021, suna cikin maye.

Jami’an tsaro sun cimma wa daliban ne yayin da suke tsaka da lalata a cikin wata maboyar daji da ke yankin Makuyu kusa da wata matsaya bayan rufe makarantarsu domin hutun Disamba.

Kalli hotunan da aka yada ta yanar gizo na daliban:

Dalibai masu group sex
Daliban da aka kama, an kulle su a ofisoshin ‘yan sanda na Makuyu da Kenol. 

Hotunan da aka yada ta yanar gizo sun nuna daya daga cikin daliban yana tofa albarkacin bakinsa a kasa bayan an kai shi ofishin 'yan sanda na yankin.

Sai dai daya daga cikin daliban har amai ya kwarara a cikin ofishin ‘yan sanda na Makuyu bayan da aka kaishi ofishin.
Labari na baya Labari na Gaba