Gwamnatin jihar Nasarawa ta haramta amfani da kuma sayar da gawayi a jihar a wani mataki na kare muhalli. 

Buhunhunan Gawayi
Buhunhunan Gawayi

Babban sakataren ma’aikatar muhalli da albarkatun kasa ta jihar, Mista Aliyu Agwai ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Lafiya bayan taron tsaftar muhalli na watan Disamba na shekarar 2021.

A cewar Mista Agwai, haramcin ya zama wajibi idan aka yi la’akari da irin illolin da amfani da gawayi ke haifar wa ga lafiyar dan Adam da kuma muhalli.

Ya bayyana cewa amfani da gawayi da kumar sayar da shi hakan ya kara assasa matsalar sare itatuwa a jihar wanda hakan ke haifar da dumamar yanayi da sauran hadurran muhalli.

Sakataren ya kuma gargadi masu sayar da gawayi da su daina sana’ar ko kuma su fuskanci hukunci.

Sai dai Mista Agwai ya yabawa mazauna jihar bisa yadda suka lamunce wa aikin tsaftace muhalli duk da sauyin da aka samu a ranaku sakamakon bikin Kirsimeti da ke tafe.

An toshe hanyoyin shiga Lafia babban birnin jihar Nasarawa domin daidaita zirga-zirga har sai an kammala atisayen.

A halin da ake ciki, Kotun tafi da gidanka da ke kula da shari’o’in tsaftace muhalli ta gurfanar da mutane 32 da ake zargi da kama su a yayin da suke gudanar da kasuwancinsu na zaman kansu cikin sa’o’in atisayen.

Alkalin kotun, Abdullahi Lande, ya yanke hukuncin daurin watanni 6 a gidan yari tare da yanke wa wadanda suka karya hukuncin tarar tsakanin N5,000 zuwa 50,000. Kamar yadda Radio Nigeria Kaduna ta ruwaito
Labari na baya Labari na Gaba