Jami’an tsaro na farin kaya, SSS, sun gayyace wani mai gabatar da zanga-zangar #NoMoreBloodShed, Ibrahim Birniwa, domin amsa tambayoyi a Kaduna.

Ibrahim Birniwa
Ibrahim Birniawa

Daya daga cikin wadanda suka gudanar da zanga-zangar ta kasa Rahma Abdulmajid, ta tabbatar da gayyatar  ‘dan gwagwarmayar ta yi wa jaridar DAILY NIGERIAN, inda ta ce “wani daya daga cikin mu shi ne hukumar SSS ta gayyace shi saboda zanga-zangar adawa da rashin tsaro.

A ranar Juma’a ne hukumar ta gayyaci daya daga cikin masu zanga-zangar a Kano, Zainab Ahmed, domin amsa tambayoyi kan yadda ta shiga zanga-zangar adawa da rashin tsaro da kisan gilla da ake yi wa talakawa a sassan Arewa da dama.

Bayan wasu awanni a hannun jami’an DSS, Ms Ahmed ta sanar da cewa ba za ta ƙara shiga zanga-zangar ba.

A ranar Asabar da yamma, hukumar ta gayyaci Mista Birniwa ofishinta na Kaduna domin amsa tambayoyi kan kiran zanga-zangar adawa da Shugaba Muhammadu Buhari kan matsalar rashin tsaro.

Mista Birniwa ya rubuta a shafinsa na Facebook da harshen Hausa cewa: “Yaushe za mu gudanar da babbar zanga-zangar adawa da Buhari ne? Me muke jira?”

Bayan gayyatar, Mista Birniwa ya goge sakon kin jinin Gwamnatin Buhari daga shafinsa sa na Facebook.

A ranar Juma’ar da ta gabata ne wasu matasa suka mamaye titunan wasu garuruwan Arewa saboda kashe-kashen da ake yi a yankin.

Duk da cewa a halin yanzu Najeriya na fama da matsalar rashin tsaro, ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda sun zafafa kai hare-hare a arewacin kasar duk da kokarin da gwamnati ke yi na dakile su.

Masu zanga-zangar wadanda ke dauke da alluna, sun shirya zanga-zangar ne a lokaci daya a jihohin Kano, Bauchi, Zamfara, Sokoto da Abuja.
Labari na baya Labari na Gaba