A wata jami'ar kasar Amurka mai suna Northwestern University wasu injiniyoyi da ke a jami'ar sun kirkiro wata kyamara mai gani har hanji ko in ce madaukar hoto mai ganin abinda ba'a gani.

Kyamarar da ke gani har hanji
Kyamarar da ke gani har hanji, Hoto: northwestern university

Ita dai irin wannan kyamara na da zuzzurfan karfin gani wanda har ta kai daga nesa tana iya ganin komai na cikin fatar mutum, kwakwalwarsa, kwanan jikin gini, asalin abubuwan da ke cikin hazo da sauransu.

Irin wannan fasahar ta yi shura a cikin fina-finan almarar kimiyya wato sci-fi movies amma a zahirance babu ita sai a wannan karon aka samu damar kirkirota a jami'ar Northwestern.

Kyamarar ta dogara ne da tsarin ɗaukar haske mai suna "Synthetic Wavelength holography," a cewar injiniyan jami'ar a cewar wata sanarwar labarai daga jami'ar Nortwestern.

Kamar yadda mujallar Futusim ta ruwaito, kyamarar tana aiki ta hanyar watsa hasken Laser akan abubuwan ɓoye, sa'an nan ta kuma mayar da shi zuwa kyamara, inda AI (Artificial Intelligence) ke sake gina siginar don nuna abin da ke ɓoye.

Me Zaka ce Game da Wannan Labari?

Labari na baya Labari na Gaba