Jaafar Jaafar ya bayar da kyautar Naira Miliyan Daya (N1m) domin a biyawa talakawa kudin tiyata, magani, da kuma kudin makaranta.

Ja'afar Ja'afar
Dan jarida Ja'afar Ja'afar

Sama da mutane 40 ne da suka fito daga sassa daban daban na jahar Kano Jaafar ya taimaka musu domin samun lafiya da kumailimi. 

Wasu daga cikin wadannan mutanen tiyata za a yi musu kuma an dade da saka lokacin amma ba su samu kudin ba, wasu kuma magunguna a ka rubuta musu amma babu kudin siya , wasu dalibaine na manyan makarantu za su biya kudin makaranta amma ba su da shi.

A kwanakin baya ne dai wata kotu ta umarci Gwamnan Kano da ya biya Jaafar Naira dubu dari takwas (N800,000) sabo da 6ata mishi lokaci da gwamnan ya yi akan shari'ar da ta shafi bidiyon dollar. 

Bayan kar6ar wannan kudin ne sai Jaafar ya cika Naira dubu dari biyu (N200,000) su ka zama miliyan daya, ya kuma mikasu ga sashen Inda Ranka na Freedom Radio domin a za6o daga cikin mabukata da su ke zuwa neman taimako akan matsalolin lafiya da na ilimi, a share musu kukansu.

Kar dai mu manta cewar yanzu haka Jaafar da iyalansa su na gudun hijira a kasar Birtaniya sakamakon barazana da ya sha fama da ita akan fallasa cushe-cushe.

Kuma kowa ya san yadda rayuwa ke da tsada a Birtaniya amma Jaafar ya ce ko Naira daya ba zai ci daga wannan kudin ba.

Mu na addu'ar Allah Ya saka masa da alkairi, Ya kuma bashi nasara a wannan gwagwarmaya da ya ke yi. Daga Kabir Dakata.

Labari na baya Labari na Gaba