A ranar talata ne wasu jami'an Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta'annati (EFFC) suka yi ram da Femi Fani Kayode, tsohon ministan sufurin jiragen sama.

Femi Fani Kayode
Femi Fani Kayode (FKK)

Kamar yadda rahotanni suka tabbatar, shi wannan lauya kuma tsohon ministan sufuri, Kayode an kama shi ne bisa zargin yin magudi da kuma bayar da jabun takardu a jihar Legas.

Jaridar Daily Post ta ruwaito cewa, an ce an garzaya da shi ofishin hukumar yaki da cin hanci da rashawa da ke Jihar Legas.

Kazalika kakakin Hukumar, Wilson Uwujaren, shi ne ya tabbatar wa Jaridar Aminiya kamun Fani-Kayode a yau talata.
Me Zaka ce Game da Wannan Labari?

Labari na baya Labari na Gaba