A karshe dai kotu ta yankewa biloniyan mai garkuwa da mutane, Chukwudimeme Onwuamadike wanda aka fi sani da Evans hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Evans the Kidnapper
Evans the Kidnapper

Rahoton ya kara da cewa,  Evans ya musanta laifin da kotun ke tuhumarsa da shi na aikata laifin garkuwa da mutane.Babbar kotun Igbosere da ke jihar Legas ce ta yanke hukuncin a jiya Alhamis, 24 ga watan Nuwamba, 2021.

Daga cikin laifukan da aka tuhumci Evans akwai, yunkurin yin garkuwa da shugaban Kamfani Young Shall Grow Motors, Mista Vincent Obianodo.

Sauran tuhume-tuhumen da ake tuhumarsa sun hada da hada baki, satar mutane da kuma mallakar makamai ba bisa ka'ida ba

An kama Evans ne tare da wasu mutane uku da ake tuhuma Joseph Emeka, Chiemeka Arinze, da kuma Udeme Upong.

Waiwaye

A shekarar 2013 rundunar yan sanda ta bayyana Evans a matsayin wanda hukumar ke nema ruwa-a-jallo bayan ya yi yunkuri sace Mista Vincent Obianodo.

Kamar yadda bincike ya tabbatar, Evans ya shafe sama da shekaru 5 ya aiwatar da aiyukan garkuwa da mutane kafin dubunsa ta cika.

Rundunar Intelligence Response Team (IRT), karkashin jagorancin D.C.P Abba Kyari sune suka kama Evans a shekarar 2017.

Sai dai yanzu haka, lauyan miloniyan mai garkuwa da mutane, Evans, ya sha alwashin daukaka kara biyo-bayan yanke wannan hukuncin.

Labari na baya Labari na Gaba