Adadin yawan mutunen da suka rasa rayukansu a rushewar dogon gini mai hawa  21 a jihar Legas ya tashi daga 22 suwa 36.

An fitar da wannan jawabin ƙidaya ne a ranar litinin, daga cikin mutum 36, guda mata ne sauran 33 maza ne.

Dandazon al'umma a wurin rushewar gini a Legas

Ko'odinetan hukumar bada agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA) a shiyyar Kudu maso Yamma, Ibrahim Farinloye shine ya fitar da sanarwar. Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito 

Ya ce daga cikin mutane tara da aka ceto, ɗaya mace ce yayin da wasu takwas kuma maza ne.

"A cikin waɗanda suka tsira, muna da mace ɗaya da namiji takwas.  Daga cikin waɗanda suka mutu, muna da mata uku da gawarwakin maza 33."

 "Har yanzu ana ci gaba da aikin ceto kuma ƙarin mataimaka sun shiga ƙungiyar ceton," in ji shi.

Ginin da ake ginawa a titin Gerrard da ke unguwar highbrow a Legas ya ruguje ne a ranar Litinin ɗin da ta gabata.

Me Zaka ce Game da Wannan Labari?

Labari na baya Labari na Gaba