Rahotanni daga can Jihar Akwa-Ibom sun tabbatar da rasuwar wani mutum ya na tsaka da taushe yam mata biyu a cikin gidansa kamar yadda jaridar Nigerian Tribune ta ruwaito.

Couple on Bed
Image source: Alamy.com

Marigayin ya ja yam matan gidansa don lalata da su, bayan ya yi musu alkawarin zai ba su aiki a NIPOST muddin suka ba shi hadin kai.

Duk da an sakaya sunan mamacin, amma dai kwakkwarar majiya ta tabbatar da shi dan kabilar Igbo ne, kuma ajali ya yi kiransa ne ya na tsaka da aikata masha'a da yam matan biyu.

"Mutumin ya rasu ne sakamakon wata gajiya da ta taso masa bayan ya kammala lalata da yam matan biyu da ya yi musu alkawarin samar musu aiki a NIPOST."

"Rundunar yan sanda ta gano gawarsa ne da misalin karfe 3 na safe, lokacin da suka yi bincike a gidansa, sun kuma yi kacibus da yam matan biyu wadanda su ka ce mamacin ya kawo su sun kwana gidansa."

Da aka tuntubi kakakin rundunar yan sandan jihar Akwa-Ibom, SP Odiko Madcon ya tabbatar da aukuwar lamarin.
Labari na baya Labari na Gaba