Mahaifin wani matashi ya aikashi lahira bayan ɗan nasa na cikinsa ya yi masa barazanar kisa.

Wannan lamari dai ya faru ne ranar Alhamis, a can Jihar Enugu, inda wani magidanci mai suna Ikechukwu ya kashe ɗansa mai shekaru 32.

Nigeria Police Force
Nigeria Police Force Logo

Mahaifin ya yanke wannan ɗanyen hukunci akan ɗan nasa bisa bargin cewa ɗan ya masa barazar kisa.

Kazalika Mahaifin ya ƙira shugaban kauyensu da kuma shugaban ƴan Bijilanti na ƙauyen don su kawo masa ɗauki.

Bayan sun isa gidan nasa, sai ya ce musu kama ɗan su ɗaure masa shi, suna ɗaure shi mahaifin ya kaftarawa ɗan nasa sara da gatari a gadon baya.

Kafin gari ya waye rai ya yi halinsa, mahaifin ya kira jama'a don a binne gawar ɗan nasa.

Da aka tuntunɓi kakakin rundunar ƴan sandan jihar, Daniel Ndukwe ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Haka kuma ya tabbatar wa da menam labari cewa; tun daga kan mahaifin yaron, shugaban kauyen nasu da shugaban ƴan bijilan duk jami'an tsaro sun yi ram da su.

Kuma nan ba da jimawa ba, za'a tasa ƙeyarsu gaban kuliya don girbar abinda suka shuka kamar yadda jaridar punchng ta ruwaito.

Me Zaka ce Game da Wannan Labari?

Labari na baya Labari na Gaba