Har kawo zuwa yanzu jama'a na ta cece-kuce game da dakatar da shirin wasan kwaikwayon nan mai dogon zango mai suna A Duniya, da Afakallah ya yi.

Naburaska da Afakallah
Mustapha Naburaska da Afakallah

Hukumar tace fina-finai reshen jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Afakallah, a kwanakin baya ta bayar da umarnin dakatar da ɗaukar shirin film ɗin A Duniya, sakamakon wasu dalilai na ta na raɗin kanta.

To sai dai, ko me yasa hukumar ta aiwatar da wannan ɗanyen hukunci?.

"Saboda hukumar na zargin film ɗin A Duniya ya na baiwa ƴan shaye-shaye ko masu garkuwa da mutane dama su ci karensu babu babbaka".

Shi dai wannan shirin (A Duniya) jarumi Tijjani Asase ne ke ɗaukar nauyinsa tare da bayar da umarni, kuma film ɗin nasa ne, ana haska shi ne a tashar youtube ta Zinariya Hausa Tv.

Har yanzu mai shirya shirin (Tijjani Asase) bai fito fili ya yi tsokaci game da wannan dakatarwa da Afakallah ya yi musu ba.

Sai dai daga cikin abokan sana'arsa, mun ci karo da wani faifan bidiyo da ya karaɗe kafafen sada zumunta, a cikinsa jarumi Mustapha Naburaska ya yiwa Afakallah wankin babban bargo akan dakatar da shirin.

Kalli cikakken bidiyon da Mustapha Naburaska ya sulluɓe Afakallah akan dakatar da shirin A Duniya ta hanyar nuna rashin goyon bayansa.

Jarumin ya wallafa wani faifan bidiyo a shafinsa na Instagram inda ya bayyana yadda yanayin film yake da kuma nuna rashin jin daɗinsa da kuma rashin adalcin da aka yiwa masu yin film din.

To sai dai abinda jama'a da dama ba su gane ba game da irin waɗannan fina-finan, da fari za'a fitowa da duniya irin ta'annatin da ƴan daba, ƴan ta'adda da sauran masu muggan laifuka su ke yi wa al'umma.

Kana daga baya kuma, sai a nuna yadda jami'an tsaro suka yi maganinsu.

Me Zaka ce Game da Wannan Labari?

Labari na baya Labari na Gaba