A ranar litinin, Ƙungiyar Mafarauta tare da Hukumar ƴan banga ta jihar Kogi ta kai samame wata maɓoyar masu garkuwa da mutane.

Inda ta yi nasarar damƙe dukkanin masu garkuwa da mutanen da ke maɓoyar, sannan ta ceto waɗansu fulani su uku da ke tsare a hannun masu garkuwan da mutanen.

Jihar Kogi
Jihar Kogi

Rahotanni sun bayyana cewa, fulanin da aka ceto yara ne ƴan ƙasa da shekaru 18, mazauna yankin Chikara ne, da ke kan hanyar Lokoja zuwa Abuja.

Kana, masu garkuwa da mutanen sun sace yaran fulanin kwanki 13 da suka gabata daga yankin Chikara.

Mai magana da yawun ƙungiyar mafarautan, Abdullahi Yahaya, ya bayyana cewa fulanin da aka kuɓutar suna cikin ƙoshin lafiya, sannan sun miƙa masu garkuwan da suka kama tare da makamansu ga jami'an tsaro.

Yahaya ya kuma yabawa gwamnatin jihar da kuma Kwamishinan ma'adanai, Engr Bashir Gegu, kan tallafa musu wajen samar da dabaru daƙile muggan laifuka a jihar. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.

Labari na baya Labari na Gaba