Gwamnatin Ƙasar Jamus ta gwangwaje hukumar tsaro ta DSS da sauran hukumomin tsaron ƙasar Najeriya kyautar motoci guda goma goma sabbi katangal.

Jamus ɗin ta bayar da waɗannan kyaututtuka ne ta hannun hukumar ƴan sanda masu daƙile aikata manyan miyagun laifuka (BKA) jiya a jihar Legas.

DSS
Department of State Services

Yayin gabatar da kyaututtukan, wadda aka gudanar a Germaine Auto Center, Lekki, Legas. Jakadan Janar na Tarayyar Jamus a  Lagos, Dr. Bernd von Muenchow-Pohl, ya miƙawa hukumomin tsaro sama da motoci goma goma.

BKA hukuma ce ta tarayyar Jamus da ke da alhakin yaƙi da tawaye da ta'addanci na duniya, fataucin miyagun ƙwayoyi, fataucin bil adama, aikata laifuka ta yanar gizo, da laifuka ciki har da satar mutane da fashin teku.

Hukumomin da suka amfana wannan kyaututtuka na motoci ƙirar Toyota Hiace sun hadar da hukumar DSS, NAPTIP, EFCC, NPF da kuma NDLEA.

Wakilan da suka karɓi motocin bas din a madadin hukumominsu shiyyar Legas sun haɗar da Daraktan DSS, Mista Egbunu J. Yusuf; Mataimakin Kwamandan EFCC, Emeka OOkonj; Shugaban NAPTIP, Ganiyu Aganran;  DCGN, NDLEA, Adeyemi Adeofe;  da DCP na NPF Tunji Disu.

Labari na baya Labari na Gaba