Labarin wata tsohuwa ƴar shekara 70 ya karaɗe kafafen watsa labari bayan wani rahoto ya tabbatar da tsohuwar ta haifi ɗanta na fari.

Wannan abin al'ajabi dai ya faru ne a wani ƙauye da ake kira Mora, da ke can Gujarat ta Ƙasar Indiya.

Tsohuwar Maijego
Tsohuwar maijego

Tsohouwar mai shekaru 70 ta haifi santalelen ɗanta na farko a haihuwarta ta farko a ƙauyen Mora da ke Gujarat.

Yanzu haka an shirya wani gagarumin bikin don taya Jivunben Rabari da mijinta mai shekaru 75, Maldhari murnar zama ɗaya daga cikin tsofaffi uwaye na farko a duniya.

Duk da cewa, sabuwar mai jegon uwar ta yi cikin ne ta hanyar IVF (Ma'ana ta hanyar yin allurar gaurayayyen mani a mahaifa).

Iyayen sun nuna yaron ga manema labarai, kodayake Rabari ta ce ba ta da ID don tabbatar da takamaiman shekarunta, amma ta ce aƙalla shekarunta sun kai 70, wanda zai sa ta zama ɗaya daga cikin tsofaffin uwaye na farko a cikin duniya.

Rabari da Maldhari sun yi aure shekara 45 da suka gabata kuma sun yi iya iyawarsu don samun haihuwa shekaru da yawa amma abun ya ci tura.

Za su iya samun ɗa ta hanya ɗaya wato hanyar IVF, wanda zai iya tasiri bayan karshen jinin al'adar Rabari.

Kalli hotunan:
Likitan dangin su, Naresh Bhanushali ya ce "daya daga cikin mafi karancin irin haihuwar da na taɓa gani."

Ya kara da cewa: "Lokacin da suka fara zuwa wurinmu, mun gaya musu cewa ba za su iya samun ɗa a irin wannan tsufa da suka yi ba, amma suka nace."

"Sun ce da yawa daga cikin dangin su ma sun yi hakan.  Wannan yana daya daga cikin h mafi karancin lokuta da na taba gani."

Me Zaka ce Game da Wannan Labari?

Labari na baya Labari na Gaba