Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya aike da tsatstsauran gargadi ga 6an bindiga, yana mai cewa "Agogon halakarku juyawa ya ke, ba za ku samu mafaka ba."

Buhari ya fadi haka ne yayin da yake mayar da martani kan kisan da aka yi wa sama da mutane 60 a garin Goronyo da ke jihar Sakkwato a ranar Lahadin da ta gabata.

Muhammadu Buhari
Muhammadu Buhari

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Garba Shehu, babban mataimaki na musamman ga shugaban ƙasa kan harkokin yaɗa labarai ya fitar a ranar Litinin.

Shugaba Buhari ya ce "Lallai kwanakin ƴan bindigar sun ƙare saboda ƙarfin sojan da sojojin mu ke samu ta hanyar sayen manyan kayan aiki da muke tura musu"

A cewarsa, "'yan fashin suna zaune ne a cikin aljannar wawa ta rashin iyawa, amma da sannu gaskiya za ta bullo garesu cikin wahala fiye da da."

Shugaba Buhari ya kara da cewa “a halin yanzu‘ yan bindigar na cikin matsanancin matsin lamba saboda tsananin kakkabesu da kuma ci gaba da kai hare-hare ta sama da ta kasa da suke sha a maboyar su daga jami’an tsaron mu.

“Harin matsorata da barayin ke kaiwa kan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, na nuna matakin masu garkuwa da mutane a karkashin matsin lamba. Amma ba za su sami inda za su buya ba kuma jami'an tsaron mu ba za su yi kasa a gwiwa ba a wannan farmakin na yanzu don fatattakar wadannan mugayen makiyan bil'adama, "in ji Shugaban.

Ya yi kira ga dukkan 'yan Najeriya "kada su yanke kauna saboda wannan gwamnatin ta himmatu fiye da kowane lokaci don kare' yan Najeriya daga gungun masu aikata miyagun laifuka da ba sa girmama darajar rayuwar dan adam."

Shugaban ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan wadanda harin Goronyo ya rutsa da su sannan ya yi kira ga jama’a da su ci gaba da hakuri da irin salon da sojoji ke bi kan yadda za a iya kai wa wadannan ‘yan bindiga hari.”
Me Zaka ce Game da Wannan Labari?

Labari na baya Labari na Gaba