Fitaccen shehun malamin nan mai bada fatawa ta addinin Islama mazaunin birnin Kano, Dr Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo ya maidawa masu aibata yan hisbah martani.

Shehun malamin ya yi magana dangane da yadda mutane ke ta yada jita-jita cewa, su jami'an hisbah yayan talakawa kadai suke kamawa yayin da suka yi ba dai-dai ba, kamar shigar bidala, askin banza da sauransu.

Dr. Sani Umar R/Lemo
Dr. Rijiyar Lemo

Su kuwa yayan masu hannu-da-shuni yan hisban ba su damke su su hukuntasu, ko da kuwa sun aikata laifuka wadanda suka sabawa addini, misali sa kaya masu fidda tsiraici, askin banza da sauransu.

Ya kara da cewa, duk wanda ya ke irin wannan ikirari to da alamu bai san shari'a ba.

Malamin ya ce ita dama ka'idar shari'a, Allah ba ya kama mutum akan abin da bai aikata ba, kazalika idan dan talaka na sabawa Allah aka hana shi ai gata aka yi masa.

Kalli cikakken bidiyon da shi Dr. Rijiyar Lemo ya fadi wannan magana, domin jin asalin abinda malam ya fadi da bakinsa.

Kamar yadda mujallar Hausaloaded ta ruwaito, malamin ya kuma bukaci al'umma su yiwa yan hisbah fatan alkhairi tare da yi musu addu'ar Allah ya kara musu kwarin guiwa wajen aiwatar da irin ayyukan da suke yi.

Malamin ya bayyana cewa, dama shi sabon Allah da kadan-kadan ya ke yaduwa cikin ak'umma wadda ya ke zama wata masifa daga baya, Allah ya yi mana maganinta ameen.
Me Zaka ce Game da Wannan Labari?

Labari na baya Labari na Gaba