Kasar bakaken fata, Afirka ta Tsakiya ta zo takanas-ta-kano har gida ta lallasa Najeriya da ci-daya-ba-ko-daya a wasan kofin kwallon kafa na duniya

A wasan kofin duniya da ake kan bugawa tsakanin manyan kasashen duniya, Kasar Najeriya ta sha kashi hannun kasar Afirka ta Tsakiya.

Najeriya da Afirka ta Tsakiya
Hoto: jaridarmikiya.com

Da farko abu rimi-rimi kamar Najeriya za ta haife da mai idanu a wasan, yan wasan Najeriya suka yi ta kai hare-hare, amma ina yau ba sa'a.

Ana tsaka da taka leda Kasar Afirka ta Tsakiya ta yi wani kukan kura ta ce, kai! ba'a san maci tuwa ba sai miya ta kare.

Nan da nan yan wasan Afirka ta Tsakiya suka zurawa Najeriya kwallo daya a raga, ita kuwa Najeriya har aka tashi ba ta zura ko daya ba.

Wannan ci-daya mai ban haushi har gida Jihar Lagos kasar Afirka ta Tsakiya ta zo ta yiwa Najeriya shi.

Nan da kwanaki uku, Najeriya za ta je kasar Afirka ta Tsakiya domin su sake fafatawa a wani sabon wasan.
Labari na baya Labari na Gaba