Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya gargadi 'yan Najeriya kan daukar makamai don kare duk wani dan siyasa gabanin zabe ko lokacin zabe.

Makinde, wanda yayi magana a jihar Legas ranar Asabar, ya lura cewa babu wani dan siyasa da zai iya bayar da rayuwarsa don kare rayuwar matasa.

Seyi Makinde
Gwamnan Oyo, Seyi Makinde

Ya gargadi ‘yan Najeriya, musamman matasa da kada wanda ya yi ganganci ya rasa ransa saboda goyon bayan‘ yan siyasa.

Makinde, wanda yayi magana yayin bikin ɗaurin auren ɗaya daga cikin yayan tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya shawarci mutanen da ke yaƙi akan siyasa da addini da su sake tunani.

Ya shawarci wadanda ke da niyyar mutuwa saboda 'yan siyasa da su canza tunani suma.

Daga nan ya yi gargadin cewa yayin da Najeriya ke tunkarar babban zaben 2023, kada wanda ya yarda ya yi fada ko ya mutu saboda wani dan siyasa.

“Idan kuka kalli tsoffin gwamnonin a jihar Ekiti, sun yi mulkin jihar amma hakan bai hana su canza jam'iyya ba. Don haka, masu son mutuwa saboda mu 'yan siyasa, ku yi hattara.

“Siyasa ba wani abu bane da zai sa kowa ya rasa ransa. Muna kusantar lokacin zaben, kuma ina so in yi amfani da wannan dama don roko gare ku duka yan Najeriya.

“Idan kuma kuka kalli wannan auren, ango da amarya sun fito ne daga dangin Kiristoci da Musulmi. Don haka, mutanen da suma suke son yin faɗa koyaushe akan dalilan addini yakamata su sake yin tunani.

“Ina so in taya Olamide da Oluwalonigba murna. Wannan shine farkon tafiya kuma ina addu'ar Allah ya basu zuriya dayyiba ”.

Me Zaka ce Game da Wannan Labari?

Labari na baya Labari na Gaba