Rundunar ƴan sandan jihar Katsina, za ta gurfanar da wata matashiya a gaban kuliya  kan zargin ta na yi wa ƴan bindiga leken asiri.

Matashiyar ƴar shekara 25 mai suna Rashida Hussaini ana zargin ta da aikata aiyukan da suka shafi fashi-da-makami tare da karya dokar hana ƙalubalen tsaro da gwamnan jihar ya rattaɓawa hannu kwanan nan.

SP Gambo Isah
SP Gambo Isah

Ƴan sandan da ke sintiri ne suka kama Hussaini akan hanyarta ta kaiwa ƴan ta'adda fetur a ranar 14 ga watan Satumba, 2021, da misalin ƙarfe 2 da rabi na dare a kan hanyar Ƙofar Guga zuwa Jibia

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, SP Gambo Isah yayin gabatar da wacce ake zargin a hedikwatar rundunar ya bayyana cewa; an kama Rashida Husaini da jakar polythene mai dauke da galan uku kowannensu cike da mai.

Yayin da ake yi masa tambayoyi, SP Isah ya kara da cewa, wacce ake zargin ta gaza iya bayar da gamsasshen bayanai a kanta. Kamar yadda Channel Television ta ruwaito.

Ta shaida wa jami'an ƴan sanda a lokacin da aka cafke ta cewa ta fito ne daga ƙauyen Daddara a ƙaramar hukumar Jibia ta jihar Katsina. Inji shi.

A cewarsa, ta canza kalamanta, inda ta ce ta fito ne daga jihar Gombe kuma daga baya ta sake canzawa ta ce ta fito daga wani ƙauye da ake ƙira Hirji a Jamhuriyar Nijar.

Don haka yanzu muna tuhumar ta a gaban kotu saboda karya dokar hana kalubalen tsaro da gwamnan jihar, Aminu Masari ya sanya wa hannu kwanan nan, da kuma hada hannu da ayyukan da suka shafi fashi-da-makami, in ji Isah.

Me Zaka ce Game da Wannan Labari?

Labari na baya Labari na Gaba