Jami'an ƴan sanda reshen jihar Jigawa sun cafke wani matashi ɗan shekara 25 saboda zargin yana yin jima'i da akuya.

Wannan matashi mazaunin kwatas din Kunnadi,  ƴan sanda sun kama shi dumu-dumu yana aikata masha'a da akuya cikin dare. kamar yadda Guardian Nigeria ta ruwaito.

Nigeria Police
Nigeria Police Force Logo

Kamar yadda Shiisu ya bayyana, ya ce ƴan sandan da ke sintiri sun kama wanda ake zargin da misalin karfe 1 na dare a cikin garin Gwaram.

Da misalin ƙarfe 1 na dare, ƴan sanda daga Hedikwatar Gwaram, yayin da suke sintiri a ciki Gwaram da kewayenta, sun kama matashi ɗan shekara 25 mai suna Nasiru Muhammad mazaunin unguwar Kunnadi, ya na tsaka da yin jima'i da akuya, in ji Shiisu.

Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Jigawa, Shiisu ya ƙara da cewa ana gudanar da bincike, bayan haka wanda ake zargi  za a gurfanar da shi a gaban kotu domin girbar abinda ya shuka.

Me Zaka ce Game da Wannan Labari?

Labari na baya Labari na Gaba