A ranar labara, Majalissar wakilai ta buƙaci Gwamnatin Tarayya ta yi gaggawar magance kisan jahilcin da ake yiwa ƴan Najeriya waɗanda basu-ji-ba basu-gani-ba a jihar Filato.

Wannan ƙudiri dai mai girma Yusuf Adamu Gagdi ne ya shigar da shi, kuma tuni majalissa ta zartar da ƙudirin nasa.

House of Reps, Nigeria

Idan ba'a manta ba, kwanan nan ƴan majalissa suka koma zaman majalissa bayan hutun watanni biyu da suka yi na shekara.

Har ila yau, Gagdi ya yabawa gwamna Simon Lalong kan ɗaukar ƙwararan matakai waɗanda suka hana haɓɓakar ramuwar gayya akan hare-haren da aka kai ta hanyar shigar da jami'an tsaro lamarin don maido da zaman lafiya a yankin da ake rikicin.

Haka kuma Majalisar ta umarci Shugaban Majalisar, Hon. Femi Gbajabiamila ya jagoranci wata babbar tawaga ya kai ziyarar jaje ga Gwamnatin Jihar Filato ya kuma yi wa Gwamna Lalong jaje kan rayuka da kadarorin da aka rasa.

Don magance sake aukuwar lamarin, Majalisar ta baiwa INEC umarni, cikin gaggawa ta gudanar da zaɓen cike gurbin kujerar Jos ta Arewa/Bassa ba tare da bata lokaci ba.

Me Zaka ce Game da Wannan Labari?

Labari na baya Labari na Gaba