Rundunar 'yan sandan Jihar Bauchi ta tabbatar da kisan mtum guda, tare da jikkata guda da wasu 'yan bindiga suka yi.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan Jihar, Ahmed Wakili, shi ne ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya ce 'yan bindigar sun farma al'umma da safiyar ranar asabar wanda.

Bala Muhammad
Gwamnan Bauchi, Bala Muhammad

Ahmed Wakili ya ce 'yan bindigar da ba'a tabbatar da adadinsu ba sun kai harin tare da kashe mutum daya, sun raunata daya, lamarin da ya haifar da fargaba ga mazauna yankin.

"Yan bindiga sun kai hari kauyen Barshin Fulani, sun kashe mutum daya, Abubakar Muhammad, babban malami a Bauchi Polytechnic."

"An harbe shi a wuya kuma nan take ya mutu.  'Yan sandan da suka garzaya wurin da abin ya faru sun dauki Abubakar zuwa Asibitin Koyarwa na Jami'ar Tafawa Balewa (ATBUTH),  Bauchi, inda aka tabbatar da cewa ya mutu."

Me Zaka ce Game da Wannan Labari?

Labari na baya Labari na Gaba