Wani sufeton dan sanda ya sa bindiga ya harbe abokin aikinsa har lahira a Jihar Kano.

Rahotanni sun tabbatar da jami'in mai suna, Sufeto Ya'u Yakubu ya harbe abokin aikinsa, Basharu Alhassan saboda yana zarginsa da tu'ammali da matarsa.

Yan Sanda
Yan Sanda | hoto:dailynigerian.com

Wannan lamari dai ya faru ne a Karamar Hukumar Warawa, da ke Jihar Kano, inda Sufeto Ya'u ya harbe Basharu bayan sun samu sabani, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Tuni abokan aikin mamacin suka ruga da shi Wudil General Hospital, inda likitoci suka tabbatar da rasuwarsa.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan Jihar Kano, Abdullahi Kiyawa, shine ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Sai dai ya musanta rade-radin da ake na zargin tu'ammali da matar wanda ya yi harbin, ya ce sabani ya shiga tsakani Sufeto Ya'u da Basharu sakamakon canjin wurin aiki.

Kamar yadda Kiyawa ya bayyana, Sufeto Ya'u ya fusata ne sakamakon dariyar da Basharu ya rinka babbaka masa saboda an masa sauyin wajen aiki daga Karamar Hukumar Warawa.

Kazalika Kiyawa ya kara da cewa, kwamishinan 'yan sandan Jihar Kano, Sama'ila Dikko, ya bayar da umarnin a mayar da case din zuwa hedikwatar 'yan sanda domin cigaba da bincike akai.

Me Zaka ce Game da Wannan Labari?

Labari na baya Labari na Gaba