Mahukuntan Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) sun bayyana sunayen 'yan Najeriya shida, a matsayin masu tallafawa kungiyar Boko Haram.

Majalisar ministocin Hadaddiyar Daular Larabawa, a ranar Litinin ta ayyana mutane 38 da wasu kungiyoyi 15 a matsayin masu goyon bayan kungiyar da sauran ayyukan ta'addanci.

Boko Haram Vehicle | hoto:guardian.ng

Majalissar ta fitar da sunayen ne a wani kuduri mai lamba 83 na shekarar 2021

'Yan Najeriya da ke cikin jerin' yan ta'adda na Hadaddiyar Daular Larabawa sun hada da Abdurrahaman Ado Musa, Salihu Yusuf Adamu, Bashir Ali Yusuf, Muhammed Ibrahim Isa, Ibrahim Ali Alhassan da Surajo Abubakar Muhammad. 

An taba gurfanar da mutanen shida a gaban shari'a a kasar da ke yammacin Asiya.

A wani bangaren kuma, Babbar Daraktar kamfanin 9mobile ta bayyana cewa mai kula da harkokin kasuwancin kamfanin, Abdulrahman Ado Musa ba daya bane daga cikin masu daukar nauyin 'yan Boko Haram kamar yadda UAE ta fitar.

Kamfanin ya yi wannan raddi ne sakamakon ganin an saka sunan Abdurrahaman Ado Musa a kafafen yada labarai.

Daraktar kamfanin 9mobile ta bayyana Ado a matsayin dan Najeriya mai mutunci da bin doka, wanda ya ke bauta wa kasar da himma a aikin gwamnati sama da shekaru talatin kafin ya canza ayyukansa zuwa kamfanoni masu zaman kansu.

Har ila yau, wata kungiyar siyasa ta yarabawa, Yoruba Ronu Leadership Forum (YRLP), ta yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya binciki lamarin tare da gurfanar da wadanda sunayensu ya fito a jerin masu daukar nauyin ta'addancin.

A cikin wata sanarwa jiya a Ibadan, shugaban kungiyar, Akin Malaolu, ya ce akwai tambayoyi da suke bukatar amsa bayan bayyana sunan Abdulrahman Ado.

Kazalika ya kalubalanci shugaban na Najeriya da ya yi gaggawar bayar da umarnin damke wanda ake zargi don gurfanar da shi gaban Kuliya. Kamar yadda jaridar Guardian Nigeria ta ruwaito

Waiwaye

A watan Afrilu na shekarar 2019, kotun daukaka kara ta Abu Dhabi ta yanke wa Surajo Abubakar Muhammad da Saliuh Yusuf Adamu hukuncin daurin rai-da-rai, sannan aka kore su daga kasar.

Ibrahim Ali Alhassan, AbdurRahman Ado Musa, Bashir Ali Yusuf da Muhammad Ibrahim Isa kowannen su an yanke musu hukuncin daurin shekaru 10 a gidan yari, sannan kuma daga baya aka fitar da su zuwa kasashen waje.

Kotun ta same su da laifin kafa wata kungiyar Boko Haram a Hadaddiyar Daular Larabawa don tara kudade da taimakon kayan aiki ga masu tayar da kayar baya a Najeriya.

A watan Disamba na shekarar 2019, wata babbar kotun tarayya ta Hadaddiyar Daular Larabawa ta yi watsi da daukaka karar da 'yan Najeriya shida suka yi, inda ta tabbatar da hukuncin kotun daukaka kara.

Me Zaka ce Game da Wannan Labari?

Labari na baya Labari na Gaba