Yau, kuma labarin wani zababhen kansila mai siyar  da shayi muka kawo muku. Wannan labarin, Rabi'u Biyora ne, ya fara wallafa shi.

Shi dai wannan mutumin da kuke gani sunansa Hon. Dayyabu Lawan, Zababbane Kansila a Karamar Hukumar Gwarzo ta jihar Kano.

Hon. Dayyabu Lawan

Tun kafin ya zamto kansila ya ke sana'ar siyar da shayi, saboda haka bayan ya zama kansila, sai ya ga bai dace ya bar sana'arsa ta siyar da shayi ba.

Dama kuma, masu iya magana sunce, a san mutum akan cinikinsa, in ya bari to a san ya daina.

Kullum da safe Hon Dayyabu ke dora garwar shayinsa, ya ci kasuwarsa, idan rana ta daga, sai ya shirya ya tafi Sakateriya wajen aikinsa.

Da daddare ma haka ya ke dora garwar shayinsa ya dafawa matasa shayi a unguwar.

Wani mazaunin Kamar Hukumar Gwarzo, Salmanu Rabi'u Gwarzo, ya tabbatar da sahihancin labarin nan, haka kuma ya kara da cewa, shi Hon Dayyabu asalinsa 'dan talaka mai fafutukar neman na kansa.

Me Zaka ce Game da Wannan Labari?

Labari na baya Labari na Gaba