Sojoji sun yiwa wani Direba duka har sai da ya kai takarda a Jos

Karar kwana ta sa wasu sojoji sun lakadawa wani magidancin direba duka, har sai da ya ce ga garinku nan a Jos, jihar Plataeu.

Sojoji da Direba
Sojoji da kuma direban da aka kashe

Wannan lamari dai ya faru ne da yammacin ranar Juma'a, 10 ga watan Satumba, 2021 a garin Jos.

Wasu sojoji da suke aiki a yankin Farin Gada sun tsare wani direba mai suna Abubakar Sadiq gabanin cikar lokacin rufe zirga-zirga (6:00pm), inda suka lakada masa dan karen duka.

Kamar yadda sahihiyar majiya ta tabbatar, sojojin sun lakadawa Sadiq duka da sanda bayan sun bashi umarni ya fito daga motarsa.

Sojojin sai washegarin ranar suka kira iyalan Abubakar Sadiq a waya, suka ce su zo su dauki gawarshi su kaita asibiti.

Daga nan iyalan mamacin sai suka wuce da gawarsa ofishin 'yan sanda na Katako.

Mamacin dai mazaunin Anguwan Rimi ne, yana da mata daya, yara hudu, kuma shine ke kula da mahaifiyarsa marar lafiya.

Kwamandan OPSH da GOC runduna ta uku ya ziyarci iyalan mamacin ya yi musu ta'aziyya, sannan ya alwashin yin bincike akan lamarin, ya kuma kawo sojojin da suka aikata wannan danyen aiki gaban kuliya.

Kawo zuwa yanzu, ba'a binne gawar mamacin ba, saboda bincike da jami'an 'yan sanda ke gabatarwa.

Madogarar wanna labari: Badawiyyah Ahmad Mu'azu ita ce ta wallafa labarin a wani post a kafar sada zumunta ta Facebook a harshen turanci.

Me Zaka ce Game da Wannan Labari?

Labari na baya Labari na Gaba