Wani labari da ya fito daga Jihar Ebonyi ya tabbatar da wani saurayi ya zabtare wa masoyiyarsa hannu akan yana zarginta da cin amanarsa.

Saurayin mai suna Chibiri Irem ya gutsure hannun budurwar tasa (Cinyere) ne bisa zarginta da yin soyayya da wani saurayin daban.

Nigeria Police Force
Nigeria Police Force

Kamar yadda Punch Metro ta ruwaito, Irem ya jima yana kashedi ga Cinyere a kan soyayya da wani a unguwarsu, sannan ya jima yana raba ta da samari barkatai, amma ta ki ji.

Cinyere ta yi kememe, ta cigaba da soyayyarta da wani saurayi har sai da rikici ya barke tsakaninta da Irem a ranar talata.

Fusataccen saurayin nata, Irem ya kaiwa Cinyere hari ne a wurin sayar da abincinsu lokacin suna tsaka da sallamar masu cin abinci.

Hukumar 'Yan Sandan Jihar Ebonyi ta tabbatar da aukuwar lamarin, kazalika yanzu haka Cinyere ta na asibiti ana kula da lafiyarta.

Me Zaka ce Game da Wannan Labari?

Labari na baya Labari na Gaba