Tsohon Ministan Lantarki, Sale Mamman ya bayyana rashin komawarsa gidansa (Taraba) bayan Buhari ya sauke shi daga matsayinsa.

Akwai wasu rahotanni da suke yawo cewa tsohon ministan ya fadi wan-war yayin da ya samu labarin sallamarsa daga aiki, sai a asibiti ya farfado.

Tsohon Ministan Lantarki, Sale Mamman

Sai dai a wata hira ta wayar tarho da BBC Hausa ta yi da Sale Mamman ya karyata rahotannin kaishi asibiti sakamakon samun labarin sallamarsa daga aiki.

Tsohon ministan, wanda ya yarda cewa yana fama da rashin lafiya, ya ce yana zuwa asibiti karbar magani tun karshen makon da ya gabata.

"Tun ma kafin a sanar da kora ta, na yi rashin lafiya mai tsanani. Ban ma je ofishin ba tun farkon makon da ya gabata."

"Don haka, jiya (Laraba) da yau (Alhamis) na sake komawa asibiti don a sake duba lafiyata; kuma likita ya ba bani shawarar cewa ina bukatar samun hutu, don haka na ci gaba da zama a wuri guda don in huta" in ji shi. 

"Na samu wuri don huta na sami kwanciyar hankali kuma in sha magani kamar yadda likita ya ba ni shawara. 

"Ban zauna a gida ba saboda masu zuwa yi min jaje da tayani alhini; wanda hakan zai hana ni hutawa da kwanciya a kan lokaci."

 "Amma sam ni ba a kwantar da ni a asibiti ba, kuma ban suma ba kamar yadda aka ruwaito." 'Buhari ne da kansa ya fada min labarin tsige ni ta waya'

Mamman ya kuma ce a ranar Litinin da daddare, Buhari ya kira shi a waya don sanar da shi labarin tsige shi.  Ya ce shugaban ya gode masa bisa goyon bayan da yake baiwa gwamnatin sa.

"Ko an kore ni ko a'a, dole ne in yi murabus cikin shekaru biyu masu zuwa," in ji shi.

In baku manta ba, Mamman Sale shine korarren Ministan Lantarki na Kasar Najeriya, wanda Buhari ya tsige.

Sannan dama an nada shi ne shekaru biyu da suka gabata wato 2019.

Me Zaka ce Game da Wannan Labari?

Labari na baya Labari na Gaba