Fitaccen 'dan wasan hausar nan, kuma dan a-mutum tafiyar jar-hula, Mustapha Badamasi Naburaska ya ce shi kam ya cire jar hula.

Tsohon dan tafiyar akidar jar hular ya ce ya rungumi tafiyar Gandujiyya.

Mustapha Naburaska
Mustapha Naburaska

A zantarwarsa da Freedom Radio Nigeria, Naburaska ya ce, ya cire jar hula tunda ba gadarta ya yi ba.

Haka kuma, Mustapha Naburaska ya kara da cewa, duk wanda ya ganshi da hakoransa 32 ya ganshi, don haka duk wanda zai taimaki sana'arsu ta film, shi ya ke yi.

"A duk Najeriya in ka cire Legas babu inda Gwamna yake zuba ayyuka kamar Kano, mu muke yawo mun je kuma mun gani."

Me Zaka ce Game da Wannan Labari?

Labari na baya Labari na Gaba