Duba da yadda da al'ummar hausawa ke bibiyar shirin labarina, wanda Saira Movies ke shiryawa, kuma tashar Arewa24 ke haska shi.

Kamar yadda binciken da muka yi ya tabbatar mana, mutane da dama na neman bayani akan sahihin lokacin da ake maimaita shirin labarina, da kuma lokacin da ake haska shi.

Hoto: arewa24.com

Tashar arewa24 na fara haska trailer na shirin labarina tun ranar juma'a da rana.

Yadda muka bincika, tashar arewa24 na haska shirin labarina duk ranar juma'a da misalin karfe 9:00pm na dare.

Sannan tashar arewa24 na maimaita haska shirin labarina a kowacce ranar lahadi da safe.

Masu Kallo a Youtube

Hakika kamfanin Saira Movies na dora shirin labarina a youtube tun kafin tashar arewa24 ta fara haska shi, suna yin scheduling dinsa ne, sai bayan masu kallon shirin a tashar arewa24 sun gama kallonsa sannan sai kuma masu son kallonsa a youtube su samu damar kallonsa.

Abinda na ke son fadi anan shine, za ku iya daukowa ko kallon shirin labarina a tashar youtube ta Saira Movies bayyan karfe 9 na daren kowacce juma'a.

Masu samun damar kallon shirin labarina dai-dai lokacin da masu kallonsa a arewa24 ke kallonsa, sune premium subscribers na youtube, yan free sai bayan 10 na dare.

Ku kasance da dan lanjeriya domin sanin labarun finafinai, labarun jarumai, labarun shirye-shirye masu dogon zango da sauransu.
Me Zaka ce Game da Wannan Labari?

Labari na baya Labari na Gaba