A ranar alhamis ne wata Babbar Kotu da ke Zuba,  Abuja ta bayar da umarnin tsare wadansu leburori uku sakamakon samunsu da laifin satar batirin tan-tan.

Rundunar 'yan Sanda reshen Zuba ce ta gurfanar da Bulus Musa, Isaac Musa da Amos Audu dukkansu mazauna Angwan Saywa, Abuja kan aika laifin makirci, wuce gona-da-iri da kuma sata.

Kotu
Hoto: dailystarng.com

Alkalin kotun, mai shari'a Gambo Gambo ya bayar da umarnin a cigaba da tsare masu laifin a gidan gyaran hali na Suleja, da ke Jihar Neja har zuwa ranar 8 ga watan Satumba domin yanke musu hukunci.

Kamar yadda jaridar Daily Star Nigeria ta ruwiaito, wadanda ake zargin sun amsa laifin da ake tuhumarsu akai.

Kazalika lauyan masu gabatar da kara, Mista Chinedu Ogada, tun da farko ya shaida wa kotu cewa mai karar, Uchenna Ikechukwu mazauniyar Arab Quarry Aco Estate Lugbe Abuja, ta kai rahoton lamarin a ofishin 'yan sanda na Zuba a ranar 26 ga watan Agusta.

Ogada ya ce wadanda ake tuhuma din, da kuma wani mai sun Bamaiyi Massani, sun shiga ma'aikatar Arab Contractors Quarry ACode tare da sace batirin katapila wanda darajarsa ta kai Naira 250, 000.

Ya kara da cewa an kamar wadanda ake tuhumar, sannan da 'yan sanda suka bincikesu sun kwato batir din daga hannun wadansa ake tuhumar.

Ya kuma bayyana cewa laifin ya sabawa tanade -tanaden sashe na 97, 387 287 na Dokar Penal Code.

Me Zaka ce Game da Wannan Labari?

Labari na baya Labari na Gaba