Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya ce gwamnatinsa na duba yiwuwar datse hanyoyin sadarwa na Kananan Hukumomi uku da ke jiharsa.

Aminu Bello Masari
Gwamna Aminu Bello Masari

Kamar yadda jaridar This Day ta ruwaito, Kananan Hukumomin da za'a katsewa hanyoyin sadarwa sun hadar da Funtua, Malumfashi da Bakori.

Gwamnan ya bayyana aniyarsa ta daukar wannan mataki a wani yunkuri na dakile aiyukan ta'addanci a Kananan Hukumomin.

Kazalika, Gwamnan ya bayyana haka ne a ranar Litinin, 7 ga Watan Satumba, yayin kaddamar da kwamitin sa ido kan dokar tsaro.

Me Zaka ce Game da Wannan Labari?

Labari na baya Labari na Gaba