Rundunar sojin Najeriya ta kerawa sojojinta wasu irin babura akalla 200 sabbin samfur, a wani yunkuri na ta na ganin ta dakile ayyukan ta'addanci a kowanne lungu da sako na kasar.

Kamar yadda Barisa Nuradden Isma'il ya wallafa a kafar sada zumunta ta facebook, su wadannan babura na hadasu ne a babbar makerar rundunar soji da ke Kaduna.

Hoto: twitter @DejiAdesogan,  UGC

Kowanne babur ya na goyon bayan soja daya, da mazaunar bindiga daga sama, da kuma rigar harsashi daga gaba (Bullet Proof Sheet Cover).

Kalli hotunan baburan yakin:
Haka kuma da muka tsananta bincike, mun ga no cewa, su wadannan babura an sabuntasu ne daga kirar mashina CJ, zuwa na sojoji masu dauke da bindiga kirar AK-47.

Kazalika, wannan rahoto tace shi da tabbatar da shi ne daga shafin twitter na @DejiAdesogan, wanda shi ne ya fara wallafa hotunan.

Da fatan Allah (S.W.T) ya baiwa jami'an tsaron Kasar Najeriya ikon dakile dukkanin matsalolon tsaro a fadin Najeriya.

Me Zaka ce Game da Wannan Labari?

Labari na baya Labari na Gaba