Kamar yadda rahotanni daga Jihar Kaduna suka tabbatar, Jam'iyyar Gwamnan Jihar, Malam Nasiru El-rufai ta sha kaye a akwatin da ya ke kada kuri'a.

Nasir El-rufai
Gwamna El-rufa'i yayin kada kuri'a

Yau asabar ne dai aka gudanar da zaben Kananan Hukumomi a duk fadin Jihar Kaduna, sai dai Gwamnan ya gaza kawo akwatinsa ta Unguwar Sarki.

Inda jam'iyyar hamayya (PDP) ta kayar da jam'iyya mai ci (APC) kasa wanwar a zaben Kananan Hukumomi a akwatun Unguwar Sarki.

Baturen zaben Unguwar Sarki, Muhammad Sani, ya bayyana cewa kuri'u 159 kadai aka kada a gaba daya akwatun, jam'iyyar PDP ta samu kuri'u 86, APC ta samu 62.

Me Zaka ce Game da Wannan Labari?

Labari na baya Labari na Gaba