Fitaccen malamin addinin Islamar nan, Mazaunin Jihar Kaduna Sheikh Abubakar Gumi ya fadawa fulani hanyar da za su yiwa kansu gata a Najeriya.

Kamar yadda jaridar dailytrust ta ruwaito, Sheikh Gumi ya ja hankalin fulanin da su tabbatar sun mallaki katin zabe kafin zaben 2023.

Sheikh Abubakar Gumi
Sheikh Abubar Gami

A cewar malamin, mallakar katunan zabe  a garesu na da matukar muhimmanci, domin zai ba su damar zabar shugaban da suke ganin zai karesu da hakkokinsu.

A wani labarin kuma: Gumi ya je garin fulani wa'azi, ya raba musu litattafai a Jihar Kwara

Sheikh gumi ya yi wannan jawabi ne a taron da wata kungiya mai suna BILMAN, ta shiya a Kaduna domin raba abinci da dabbobi ga fulani wadanda rashin tsaro da annobar kwarona suka aukawa.

Haka kuma malamin ya shawarci fulani da su hada kansu kada su yarda wata jam'iyya ko dan siyasa yaraba su, domin yadda kabilarsu za ta iya taka muhimmiyar rawa a zaben 2023.

Kazalika malamin ya yi gargadi da fulani, musamman makiyaya mazauna dazuka da su kiyayi aikata miyagun laifuka (garkuwa da mutane da fashi).

Me Zaka ce Game da Wannan Labari?

Labari na baya Labari na Gaba