Sheikh Ahmad Gumi ya je garin fulani wa'azi, ya raba musu littafai a jihar Kwara

Babban malamin addinin islamar nan, Sheikh Dr Ahmad Gumi ya je wa'azi babban birnin jihar Kwara, ya kuma gana da al'ummar fulani.

Kazalika Malam Gumi ya kuma bayyana musu kudirinsa na gina gidauniya ta musamman wa fulanin.

Malam Gumi dai ya shahara ta fannin shiga daji ya yiwa fulanin daji, da masu garkuwa wa'azi, basu litattafan addini, da kuma gina musu burtsatsai da makarantu.

Kamar yadda hadimin malamin, Salisu Hassan Webmaster ya wallafa a shafinsa na facebook a ranar Asabar, 4 watan Satumba, Malamin ya tafi garin Ilesha domin rabawa al'ummar fulani littatafan addini. 

Dr Ahmad Gumi
Dr Ahmad Gumi

"Dr Ahmad Abubakar Mahmhd Gumi tare da tawagarsa a garin illesha, Illorin jihar Kwara."

"Muna sa ran Malam zai gana da Al'ummar Musulmai Fulani mazauna wani kauye tare da yi musu nasiha da kuma raba musu littafan addini." 

"Cikin tawagarsa akwai Professor Usman Yusuf, Sheikh Sunusi Kutama, Alaramma Muh Auwal

Alaramma Gezawa,  Mal. Murtala Abdullahi, Mal. Nasiru Ayyub, Da sauran al'umma baki daya."

"Allah muke fatan ta bada nasara ya sa a mizani ya kara iklasi, yakarbi wannan aiki ya karesu da dukkan abin ki, ya dawo da su lafiya. Amin."

Me Zaka ce Game da Wannan Labari?

Labari na baya Labari na Gaba