Shugaban Kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya yi kira ga daukacin likitocin da suke yajin aiki da su gaggauta dawowa bakin aiki cikin gaggawa.

Kazalika shugaban ya bukaci sauran ma'aikatan gwamnati masu tunanin yajin aiki a matsayin babban mataki da za su iya dauka, da su zabi sasanta batutuwan ta hanyar sulhu da sasantawa, komai kuwa irin tsawon lokacin da za a dauka.

Muhammadu Buhari
Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari

Shugaban ya yi wannan roko ne lokacin da ya karbi bakuncin mambobin kungiyar Likitocin Najeriya, NMA, a fadar gwamnati, Abuja, ranar Juma’a.

A cewar shugaban, rayukan 'yan kasa da za a iya rasawa yayin da likitoci suka tafi yajin aiki, suna da daraja sosai da gwamnati za ta iya bin duk hanyar sasantawa da likitocin don warware matsalar cikin lumana.

Haka kuma Shugaba Buhari ya ce gwamnati za ta biya dukkanin likitoci hakkokinsu da suke binta, bayan ta kammala tantance komai.

Ya kuma lura da cewa, fara aiyukan masana'antu yayin da kiwon lafiya ke cikin mawuyacin hali, ba kyakkyawan zabi bane ga kasa da 'yan kasa.

Me Zaka ce Game da Wannan Labari?

Labari na baya Labari na Gaba